Kotu Ta Soke Zaben Dan Majalisar Tarayya A Bayelsa
Kotun daukaka kara a jihar Bayelsa ta soke zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Sagbama-Ekeremor a majalisar wakilai, Fred Agbedi na jam’iyyar PDP.
Dan takarar jam’iyyar APC Michael Olomu ne ya shigar da karar.
Kotun ta kuma ajiye takardar shaidar lashe zaben da aka baiwa dan takarar PDP.
Kotun ta kuma umurci INEC da ta gudanar da wani zabe a cikin kwanaki 90 a wasu rumfunan zabe da dakunan zabe a kananan hukumomin Sagbama da Ekeremor, inda zaben ya fuskanci tashe-tashen hankula da wasu kura-kurai.