Labaran YauNEWS

Kungiyar Kwadago NLC Ta Ce Zata Saka Kafar Wando Daya Da Wike

Kungiyar Kwadago NLC Ta Ce Zata Saka Kafar Wando Daya Da Wike

Kungiyar Labour Congress, NLC, ta yi artabu da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan rushe rushen da aka yi a babban birnin tarayya, Abuja.

Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya ce an yi ruguje ruguje ne ga talakawa kamar yadda azzalumi Hitler ya yi.

DOWNLOAD ZIP/MP3

“Matsuguni yana cikin manyan bukatu na Masu karamin karfi kuma an je an ruguza masu, wato ka ce su shiga wuta kuma abin da ake kira master plan dinka yana cikin aljihunka.

“Ba wanda ya san inda babban shirin ku yake. Kuma muna fadawa duniya cewa NLC ta ja layi a kan shirin rushe rushe na Wike a Abuja, wasun su na amfani da kudaden ritayar su don fara gina kasuwanci (kuma ku rusa musu), hakan ba zai ci gaba ba”.

“Yana talauta talakawa kuma ana yin hakan ne da wani mataki na rashin hukuntawa irin na zaluncin Hitler a Jamus. Bai kamata a ci gaba da hakan ba domin yana shafar ma’aikata. Idan ka duba mutanen da ake ruguza gidajensu to irin wadannan mutane ne da ba su da gidaje na kansu”.

“Halin da Najeriya ke da shi ga jin dadin jama’a ya kare kenan, to ba haka Kundin Tsarin Mulkin kasa ya koyar ba.
ku manya a kasa baku da matsala domin arzikin kasa yana biya maku bukatun ku, kuna da ruwan ku na sha, wutar lantarki, kuna biyan kuɗin makarantar yaranku, talaka kuma koh asibitoci wadatattu an kasa samar masu. ma’aikata suna ba da gudummawar kuɗi na haraji don manufofin kasa, amma ana karkatar da su.
Don haka wannan zalunci ba zai ci gaba ba,”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button