Kotu Ta Yi Hani kan Kama Ganduje
Kotun kasa ta jihar kano ta hana Hukumar Rashawa ta jihar Kano, yan sanda, jami’in tsaro na jiha da Sibil defence daga kama tsohon gwamna na kano Abdullahi Ganduje da iyalin sa da Kuma wanda ya bada mukamai.
Dokar an bada ne wajen katse kirar ziyara da Hukumar Rashawa tayi domin ansa tambayoyi kan bidiyon dala wanda daily Najeriya ta wallafa a watan Oktoba ta shekarar 2018.
Bidiyon ta nuna Ganduje yana sanya kudade dalar America a cikin aljihunsa wanda ake zargin kudade ne na rashawa.
Ranan laraba shugaban Hukumar Rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado ya bayyana binciken su wanda sun tabbatar bidiyon Gaskiya ne.
Amma ganduje ranar Jumma’a ya nemi damar ji daga gare shi, wanda mai shari’a A. Liman ya amince da neman daman, Kuma dokar ta tsayar da kamin har Sai anji daga bakin sa.
Dokar Tace, “Dokar ta bada hani dan kama mai kare kansa ko da yardan sa, daga shiga hannun yan tsaro, da Kuma hani kan wulakanci, barazana, ko yun kurin kama shi ko iyalensa da wanda ya basu mukamai a lokacin sa na gwamna ko kwace dukiyar wani cikin su, kamin a zantar da hunkunci.
“Kuma dokar ta zauna har lokacin da za ayi zaman dan karfafa yancin sa na dan kasa wanda za ayi zaman ran 14 ga watan Yuli shekarar 2023.
“Kuma a bada takardan bincike awa 36 kamin lokacin da za a aiwatar da binciken daga yau”