Labaran Yau

Gwamnan Zamfara Ya Rage Ministiri 28 Zuwa 16

Gwamnan Zamfara Ya Rage Ministiri 28 Zuwa 16

Gwamnatin Jihar Zamfara Dauda Lawal ya saka hannu kan dokar sabon tsarin gwamnatin na gudanar da ministiri da rage yawar ta daga 28 zuwa 16.

A bayanin Sulaiman Bala Idris, Mai magana da yawun gwamna, ya tabbatar da maganan cewa anyi hakan ne dan a rage yawan ministiri da suke abu daya.

Yace gwamna sa hannu  dokar ne ranan Alhamis ofishin gwamnati na gidan gwamnati a Gusau.
Sabbin ministirin sun hada da: noma, kasafi da tsare tsare, science da taknolaji, Muhalli da Albarkan kasa, Kudade, Lafiya, kasuwanci da saka hannun jari.

Zantarwa da Al’ada, Shari’a, gidaje da cigaban birni, kananan hukumomi da masarautan gargajiya, Lamuran Addini, lamuran mata cigaban mutane, Aiki da Gine gine, Samari da wassani, Tsaro cikin gida da lamuranta.

Bayan haka gwamnatin jiha ta gaji babban Albashin Ma’aikata harda na watan Yuni.

Bayan karbar karagar mulki yayi korafi kan yawan albashi, cewa ya samu miliyan hudu ne kawai cikin asusun gwamnatin.

“Ina gudanar da ayyukan gwamnati akan bashi tunda na hau ofishin gwamna, nasamu asusun gwamnati babu kudi, asusu daya na gani mai miliyan 3 zuwa 4” ya bayyana a hirar sa da BBC.

“Yanzu ya kai wata uku bamu iya biyan Albashi ba, in ka duba hukumomin gwamnati zaka ga basu da wuta an yanke saboda basussuka da sukayi yawa.

“Jami’an tsaro akwai alawus dinsu da har yanzu bamu biyasu ba, Yanzu haka daliban sakandare basu rubuta jarabawar WAEC da NECO saboda basussukan sun kai biliyan wanda suke bin gwamnati”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button