Yan Najeriya 14 Suka Ransu A Hajjin Bana 2023
Hukumar Alhazai na Najeriya, NAHCON, ta bayyana cewa Alhazai 14 ga a Saudiyya daga farawan hajji zuwa yanzu.
Usman Galadima, shugaban gudanarwa Kuma jagoran jami’un lafiya ta hukumar Alhazai, ya bayyana hakan a wajen zaman da sukayi bayan Arafat ranan lahadi a Makkah kasar saudiyya.
Galadima ya ce rasuwan yazo daban daban ne wanda Alhazai 7 suka rasu kamin hawan Arafat, 6 Kuma sun rasu lokacin Aikin Hajji Sai mutum daya ya rasu bayan kammala hajin da akayi bana.
“Mun samu rasuwan mahajjata 6 a mashair, mutum hudu sun mutu a Arafat, mutum biyu sun rasu a Mina Sai mutum bakwai Kuma Yanzu haka an kawo mana rahoton wani ya rasu. Hakan ya hada yawan Alhazai 14 ne suka rasu.
“Hakan ya nuni da kamaimaiciya da ta faru a shekarar 2019” ya ce.
Ya kara da bayyana cewa mutum uku ne aka samu da cutar chickenpox a lokacin aikin hajji, sai Akayi gaggawan fitar dasu dan kar ya shafi wasu.
Galadima ya ce mata biyu suka haihu daya a Muzdhalifa daya a Arafat a Mina. Daya daga ciki ta haihu a hanya dayan Kuma ta isa asibitin kamin ta haihu.
Ya jaddada amfanin tantance yan zuwa hajji, da takardar lafiya medical certificate of fitness.
Yace Za fara bada rashin karfin gwiwa kan tsoffi da wanda basu da lafiya zuwa jifan shedan a jamrat saboda ci kowa.
A bayanin shugaban jirage na Hukumar Alhazai ta kasa Alhaji Goni Sanda, ya bayyana cewa za a fara dawo da Alhazai gida Najeriya ranan talata Hudu ga watan yuli.
Dokar wanda ya shigo farko shi zai fara fita yananan Zamu aiwatar zuwa komawa Najeriya.
Ya Kara bayyana cewa Gwamnatin saudiyya bata ya bar jiragen kaya Suna fita sosai ba saboda yawan jiragen dake fita Suna yawo a sama wajen maida Alhazai kasashen su. Kuma jiragen zasu tashi daga filin jirgi guda na filin jirgi na kasa da kasa na Sarki AbdulAziz dake Jiddah.
Ya ce a sati biyu na farko na safaran Alhazai, flynas zata rage aiki samo yawan jirage da ke sama, zasuyi amfani hudu cikin shida na jirage zasu yi amfani dan biyu daga ciki Suna wajen gyara da maintenance.
Kwamishinan gudanar wa na Hukumar Alhazai Alhaji Abdullahi Hardawa, yace zasu jajirce wajen lura da Alhazai wajen dokan daukan kaya a yayin dawowa Najeriya.
Ya ce shekarar da ta gabata 2022, in sallake doka, yace wannan shekarar barasu bari a karya doka, dan samun gudanar wa Mai sauki.
Yayi korafi akan dabi’un mahajjata mafi yawa mata sun fi zuwa da jakakkuwa dayawa na kaya, yace wannan shekaran barasu lamunta ba.
Ya fadawa Ma’aikatan Hukumar Alhazai na jihohi da su fadawa mutanen su. Dan a kauda duk wasu matsaloli da zasu iya haifar da rashin gudanar wa Mai tsari a filin jirgi.
“Jami’un filin jirgin sunyi korafi kan dabi’un mutane kan tahowa da kaya da yawa, wanda hakan yana saka rayuwana fasinjojin a riski wannan lokacin bara ayi kasuwan ci ba yanda aka saba.
“Da Kuma tsoron yasar da kaya masu amfani, mutane suyi kokarin sanya kayan a jiragen kaya na cargo” ya kara fadi.