Labaran Yau

Sojoji Basu Da Mafita Kan Ta’addancin Arewa Maso Yammacin Najeriya Tukunna – Shettima

Sojoji Basu Da Mafita Kan Ta’addancin Arewa Maso Yammacin Najeriya Tukunna – Shettima

Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ya nemi goyon bayan yan Najeriya in an fitar da mafitar dakile matsalar Yan Ta’adda da sauransu a Arewa maso yammacin kasar.

Daily trust ta rawaito cewa yankin Tana fuskantar kasuwan ta’addanci wanda ya hada da kisa, garkuwa da mutane da satan dabbobi da kayan abinci. Hakan ya saka mutane sun rasa gidajen zama wasu sun rasa rayukan su.

Wasu daga cikin jiga jigan su bada shawaran canza yanayin aikin da tsarin wajen kawo sabuwar mafita dan dakile matsalar.

DOWNLOAD MP3

Amma shugaban sojin kasa Major Janar Taoreed Lagbaja ya kori maganar Amnesty wato sulhu da yan Ta’adda dan neman biyan bukatar su. Hakan yana saka marasa kishin kasa su hada nasu kungiyar Suna kai farmaki wa wanda basu ji sun gani ba.

A jawabin Mataimakin shugaban kasa ranar lahadi a garin Kano, yace shugaban kasa Tinubu ya tsaya a tsaye dan canza tsarin gudanar da mulki na Zamani.

Yace babu mafitar da ake dashi na soji da zata dakile matsalar Arewa maso yamma.

DOWNLOAD ZIP

Ya ce “Matsalar ta’addan ci da muke dashi a Arewa maso Yamma ya ta’allaka ne da talauci da Kuma kebancewa. Abinda shugaban kasa yake so ya magance kenan nan bada jimawa ba. Zai bayyana mafitar.

“Sai dai in bamu so wannan matsalar ta kare, dole a samu budaddiyar mafita da kuma kulalliyar  mafita. Shugaban kasa zai bayyana Mafitar a sati  biyu masu zuwa domin kawo maslaha game da matsalar kebancewa na Fulbe. Dan samo mafita tun daga silar matsalar ta’addanci a kasar”.

Mataimakin shugaban kasa yaje kano ne domin yin Ta’aziyya wa Sarkin Bichi ALHAJI Nasiru Ado Bayero, bayan rasuwar sirikin shi Malam Imam Galadanchi.  Kuma siriki ne wa sarkin musulmi wanda suka karbi ziyarar shi, Gwamna Abba Yusuf Kabir ya jagoranci tafiyar zuwa fadar.

A gidan sarki na Kano, Sarkin Bichi ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu da mataimaki shugaban kasa Kashim Shettima. Ya Kuma da yarda dasu wajen kawo dokoki da gudanar wa wanda zai kawo cigaban kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button