Gwamnatin Kano ta maida martani wa NNPP cewa Ganduje zai bada karagar mulki cikin sauki
Gwamnatin Jihar Kano tace wa kwamitin karban mulki na jam’iyyar NNPP cewa Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje zai miqa karagar mulki cikin sauki ba tashin hankali.
Manema labarai na Daily Nigeria ranan jumma’a sun bayyana cewa gwamnati Mai ci Tana kokarin bata tsarin shirye shiryen mika karagar mulki a jihar.
Kwamishinan zantarwa da harkokin cikin gida na jihar kano Muhammad Garba, ya fada ran Asabar cewa manyan kwamitin da kananan Suna aiki ne dan samar da canjin mulkin cikin sauki.
Garba ya kori korafin da jam’iyyar PDP keyi akan gwamnati mai ci na yin abubuwa da zai bata mika karagar mulkin.
Shi kwamishinan ya bayyana cewa kwamitin manya da kanana Suna aiki tukuru dan hada kan abubuwa gwamnati tun daga department har zuwa ministri dan bada bayani ingantance, Kuma a halin yanzu an cimma aikin.
“Kwamishinan ya yi bayani kan lamarin hada bayanin cewa in sun gama hada bayanin zasu mika wa gwamnati mai shigowa akan lokacin” a yadda bayanin yazo
“Yace sun bada dama wa kwamitin gwamnati Mai shigowa ta shigo cikin hada bayanan dan nuna gaskiya a cikin aikin”.
Tunda gwamnati mai fita take da duk bayanan da ake bukata, Toh kwamitin gwamnati Mai shigowa yakamata yazama kadan. Yadda akeyi tsakanin jam’iyu biya daban daban a jihohi.
A bayanin Garba ya bayyana aikin su shine su bada rahoto tsakanin wannnan gwamnati zuwa ga sabon gwamnati ne ba su kawo wata aqida ba.
Kwamishinan ya nuna zargin NNPP kan gwamnati mai fita na kirkiro mummunan aqida ya jira sai bayan an mika karagar mulki.
Malam Garba yana Jan hankalin kwamitin gwamnati mai jiran gado dasu nisanci wata batu na hayaniya suyi aiki cikin nutsuwa dan asamu cimma buri.
Daily Nigeria ta rawaito