Labaran Yau

Kungiyar Manchester United Na Cigaba Da Shirye Shiryen Tunkarar Kakar Wasanni Mai Gabatowa

Kungiyar Manchester United na cigaba da shirye shiryen tunkarar kakar wasanni mai zuwa.

Bayan nasarar cimma yarjejeniya ta daukan Dan wasan tsakiya na Chelsea wato Mason Mount, kungiyar sun cigaba da kokarin kawo wasu yan kwallon domin ciyar da kungiyar gaba.

Tun kafin kakar wasanni na bara ta kare, masu tattaunawa akan kwallon kafa sunyi fashin baki akan abunda kungiyar Manchester United din tafi buqata.

Manchester United

Karancin yan kwallon gaba da gola Wanda yayi dai dai da zamani sune sukafi addabar kungiyar mai matukar tarihi. Kungiyar tayi yunkurin daukan shahararren Dan wasan kungiyar Tottenham wato harry kane amma abun na da matukar wuya duba da yadda mai klub din ya nuna rashin shaawarsa na siyar da Dan wasan a Ingila.

Awanni kadan da suka gabata Manchester United ta miqa tayin dola miliyan talatin da biyar ga kungiyar kwallon kafa na atalanta dake Italiya domin daukar Dan gabansu wata rasmus hojlund amma kungiyar sunyi watsi da tayin.

Zamu cigaba da zuba ido mu gani ko kungiyar zasu kara miqa wani tayin ko kuma zasu leqa wasu takwarorin nasu domin daukan yan kwallon gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button