Labaran Yau

Gada A Jihar Gombe Kan Hanyar Zuwa Bauchi Ta Karye Saboda …

Gadar Gombe ta ruguje bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, wasu matafiya sun makale bayan wata gada da ke kan hanyar Bauchi zuwa Gombe ta ruguje a safiyar

Lahadi, 13 ga watan Agusta, biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Wannan dai ba shi ne karon farko da za a wanke gadar ko wani bangare na hanyar ba bayan an yi ruwan sama.

Wakilin mu ya ruwaito cewa gadar da ake gyaran  ta ruguje har sau uku a bara.
Rugujewar na baya-bayan nan dai ta shafi hanyoyin da suka fito daga sassan kasar nan zuwa jihohin Arewa maso Gabas da suka hada da Gombe, Adamawa, Taraba da wasu sassan Borno da hanyar jihar Bauchi.
An karkatar da zirga-zirgar ababen hawa zuwa hanyar Bauchi-Darazo-Dukku-Gombe, inda aka tsawaita hanyar Bauchi zuwa Gombe da sama da kilomita 78.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button