Labaran Yau

Tinubu Ya Dawo Najeriya Dan Shirye Shiryen Karbar…

Tinubu ya dawo Najeriya dan shirye shiryen karbar mulki

Bola Tinubu, zababben shugaban kasan Najeriya ya dawo Najeriya da matarsa Sanata Oluremi, bayan tafiyan hutu da sukayi. Hukumar labarai ta kasa (NAN) ta bayyana hakan.

Tinubu wanda jirginsa ya sauka a masaukin shugaban kasa a filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja ran litinin karfe 4:30 da yamma.

Ya samu maraba da dawowa daga mabiya, da masoya, da yan jam’iyyar Apc.

DOWNLOAD MP3

Cikin wanda suka tarbeshi sun hada da Sanata Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, James Faleke, Ade Omole, gwamnan jihar pilato Simon lalong, tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomole da sauransu.

Gidan tsaro ( defense house) Tinubu zai sauka har zuwa 29 ga watan mayu, ranan da zai karba karagar mulki.

DOWNLOAD ZIP

A baya ranan 21 da watan maris, Tinubu ya fita dan hutawa a kasar faransa dan kuma tsare tsaren kamin rantsar wa cewar Mambobin APC.

“Zababben shugaban kasa ya fita a kasar ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Ikeja a jihar legas.

“Ya dau niyyan daukan hutu bayan zirga zirgan siyasa da kampen na zaben da ta gabata, ya tafi Paris da london, bayan nan ya shirya wa zuwa saudiyya dan yin umrah da yin azumin watan Ramadan” a bayanin APC PCC.

Hukumar labarai ta kasa sun bayyana cewa mabiya daga Nasarawa da Niger sun garzaya zuwa ofishin APC na Abuja central business district don tafiya tarban shi da maraba da dawowan sa.

DailyNigeria sun rawaito cewa tantancun mabiya kadai aka bari shiga tarban Tinubu da matan sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button