Labaran Yau

Kungiyar Kwallon Sawu Ta Liverpool Zata Dawo Hayyacinta

Kungiyar Kwallon Sawu Ta Liverpool Zata Dawo Hayyacinta

Klopp na shirin mayar da kungiyar sa ta liverpool zakarun nahiyar turai. Biyo bayan rashin nasara a kakar wasannin firemiya daya gabata, kungiyar ta koma ajin Europa league. Wannan ne ya janyo mahukuntan wannan kungiya sukaga yiwuwar dauko sababbin yan wasa musamman na tsakiya.

Tuni dai kungiyar ta dauki shahararren Dan wasan Brighton kuma dan kasar Argentina wato mc allister akan dola miliyan talatin da biyar.

A cigaba da wannan ginin ne kungiyar tuni ta cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta kasar jamus wato RB Leipzig akan daukar Dan wasansu mai suna dominik szoboszlai akan iro miliyan saba’in.

Ana ta rade radi akan cewa watakila kungiyar zasu taya dan wasan kasar faransa wato kylian Mbappe kafin a rufe siya da siyarwar yan wasan wannan kaka da zamu shiga.

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button