AddiniLabaran Yau

Allah Yayiwa Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Abubakar Giro Argungu Rasuwa

Allah Yayiwa Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Abubakar Giro Argungu Rasuwa

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) a Najeriya Bala Lau ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin jiya Laraba. Ya bayyana cewa, “Dukkanmu na Allah ne, kuma daga karshe zamu koma gareshi. Sheikh Abubakar Giro Argungu ya bar duniya.”

Mai girma malamin ya rasu ne sanadiyyar wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya a garin Birnin Kebbi, kuma za a yi jana’izarsa a yau Alhamis, sai dai idan Allah ya kaimu. Bala Lau ya kuma bayyana cewa za a sanar da lokacin jana’izar daga baya.

DOWNLOAD MP3

Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda dan karamar hukumar Argungu ne a jihar Kebbi, ya samu karbuwa sosai a jihohin Arewacin Najeriya inda ake jin harshen Hausa. A makon da ya gabata ma yana Kano, inda ya bude wani sabon masallaci da aka gina, wanda wani dan kasuwa Abdulkadir Rano ya bayar da tallafin kudi da masallacin a karamar hukumar Rano ta Kano.

A yayin wannan taron, ya gyara kalaman daya daga cikin takwarorinsa na Kano, Sani Ashir, wanda ya bayyana ‘yan siyasan adawa na kalubalantar zaben gwamnan Kano a gaban kotu a matsayin makiyan jihar tare da yi musu addu’ar halaka. Da yake mayar da martani, Mista Giro ya jaddada cewa, abu ne da ya dace da ‘yan siyasa su nemi hanyar shari’a don kalubalantar abokan hamayyarsu.

Idan dai ba a manta ba a shekarar 2021, a baya an yi ta rade-radin cewa Abubakar Giro ya rasu, amma shi da kansa ya fitar da wani faifan bidiyo don karyata wadannan rahotannin a waccan lokacin. Sai dai abin takaicin shi ne, a yanzu rasuwar tasa ta Gaskiya ta tabbata, bayan shekara daya da watanni tara da rasuwar abokin sa kuma malamin sa, Dr. Ahmad Bamba, a Kano.

DOWNLOAD ZIP

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button