An tabbatar Da Rasuwar Fitaccen Dan Siyasar Jahar Bauchi
Innalillahi wa Inna illaihir rajiun fitaccen dan Siyasa a Jihar Bauchi kuma jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Hassan Muhammad Sharif wanda iyalensa suka tabbatar da rasuwansa bayan samun hatsarin mota da yayi a Hanyar sa ta dawowa daga Abuja.
Sarkin Arewa ya rasune a hanyarsa na zuwa Bauchi a jiya lahadi da misalin karfe goma na dare.
Dansa mamacin ne Khalid Arewa ya tabbatar da rasuwan wanda Yace maihaifin nasa an kwantar dashi a asibiti a nan garin Akwanga na jihar Nasarawa, nan take likitotin suka tabbatar musu da cewa Ya rasu.
A yau muka samu labari daga shafin dansa khalid wanda ya tabbatar da cewa Mai Martaba Sarkin Bauchi ya umurni a sallace a yau karfe biyu rana.