Labaran Yau

Fintiri Ya Doke Binani Ya Lashe Zaben Adamawa Da Ratan Kuri’u..

Hukumar zabe ta bayyana fintiri a wanda ya lashe zaben gwamna a Adamawa

Hukumar zabe ta kasa ta bayyana sakamakon zaben Gwamna a jihar Adamawa, Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP ya lashe zaben.

In ba a manta ba, Hukumar zaben ta kara maimata zaben saboda banbancin kuri’u.

Sakamakon da ya fito ran 20 ga watan maris, Aishatu Binani na jam’iyyar APC tanada 390,285. Fintiri Kuma yanada kuri’u 421,524.

Bayan an sake zaben ranan Asabar da ta gabata, an katse hada sakamakon ranan lahadi, bayan hayaniya da ya biyo bayan bayyana Binani a matsayin Gwamna wanda ba bisa ka’ida ba.

Kwamishinan zabe na jiha, Barr. Yunusa Ari ya bayyana Binani a matsayin Gwamna a tsakiyar hada sakamakon zabe. Wanda ya sa aka katse komai.

Yau Talata, farfesa Muhammad Mele ya bayyana sakamakon zaben, Kuma ya bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben.

Gwamna Fintiri a karshe ya ci zaben da kuri’u 430,861 akan Binani mai kuri’u 396,788 a zaben Gwamna na jihat Adamawa.

ADAMAWA STATE GOVERNORSHIP ELECTION:

FINAL RESULTS TALLY

APC: 396,788

PDP: 430, 821✅

(SOURCE: INEC COLLATION)

WINNING MARGIN: 34,033 votes

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button