Cinikayyan Yan Kwallo. Salah, Mane, Lewandowski, Origi
Mohamed Salah, na dab da sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar zamansa a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool har zuwa karshen sana’arsa ta kwalllon kafa.
Real Madrid na daga kungiyoyin da ke da sha’awar tattauna batun sayen N’Golo Kante na Chelsea, idan har za a sayar da dan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara 31, a bazarar da ke tafe.
Dan bayan Chelsea dan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25, ya cimma yarjejeniya ta baka kan cewa zai koma Barcelona.
Dan gaban Bayern Munich Robert Lewandowski ya gaya wa Barcelona cewa yana son zuwa kungiyar a bazaran nan, idan har za ta ba dan wasan na Poland mai shekara 33 kwantiragin da ya wuce shekara biyu.
Dan gaban Liverpool na Belgium Divock Origi, mai shekara 26, na dab da cimma yarjejeniyar shekara hudu da AC Milan.
Erik ten Hag ya ware ‘yan wasa biyu da yake son saye idan har ya zama kociyan Manchester United, kuma dukkaninsu daga kungiyarsa ta yanzu Ajax suke – dan Brazil Antony, mai shekara 22, da kuma dan Netherlands Jurrien Timber, mai shekara 20.
An gaya wa Manchester City da Liverpool cewa su bar maganar matashin dan wasan tsakiya dan Sifaniya Gavi, mai shekara 17, saboda yana shirin kulla sabuwar doguwar yarjejeniyar zamansa a Barcelona. (90min)
Leicester na tunanin sayar da dan wasanta na tsakiya dan Ingila wanda aka yi wa kudi fam miliyan 50, James Maddison, mai shekara 25, saboda sake fasalin kungiyar a bazaran nan.