Labaran Yau

Juventus Na Shirin Sayarda Gwarzon Dan Wasansu Pogba

Juventus Na Shirin Sayarda Gwarzon Dan Wasansu Pogba

Yau shekara daya kenan bayan da pogba ya dawo Juventus daga Manchester United a kyauta, Kungiyar kwallon kafa ta Juventus dake kasar italiya ta sakawa shahararren dan wasan tsakiya na faransa wato Paul Labile Pogba farashi.

Tun bayan zuwansa kungiyar Paul pogba yayi fama da rauni wanda ya hanashi buga kwallo wajen wata shida. Dan wasan ya buga wasanni shida kacal tun bayan komawa kungiyar daga Manchester United dake kasar ingila.

Juventus Na Shirin Sayarda Gwarzon Dan Wasansu Pogba
Juventus Na Shirin Sayarda Gwarzon Dan Wasansu Pogba

Da yammacin yau ne jaridar gazetta dake italiya ta rawaito cewa kungiyar Juve ta sakawa pogba farashin iro miliyan goma.

DOWNLOAD MP3

Pogba dai yayi fama da rauni mai tsaho wanda ya saka bai halarci gasar kwallon kafa ta duniya da akayi a kasar Qatar ba a shakarar data gabata. Ciwon ya janyo masa rasa gurbinsa a tawagar kasarsa ta faransa.

 

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button