Labaran Yau

Kotu Ta Hana Gwamnatin Kano Rusa Gine Gine

Kotu Ta Hana Gwamnatin Kano Rusa Gine Gine

Kotun gwamnatin tarayya ta kasa a Kano ta tsaida tsarin rushe rushen gine ginen da akayi a polytechnic na jihar Kano ta BUK Road.

Kamar yanda Labaranyau ta samu jawabi daga channels TV an samu rahoton cewa Alkalin, Simon Akpah, ya bada Umarnin bayan yanke hunci da yayi kan karar da dan jihar kano ya kai, Saminu Mohammad ta hannun lauyansa Nasir Aliyu.

Alkalin ya hana gwamnati da karta rusa dukiya ta gine gine na No. 41 da 43 Salanta, a hanyar BUK Road, Kano.

Wanda hanin ya isan ma sun kunshi, Atoni Janar na jihar Kano, gwamnan jihar Kano, gwamnatin kano. Da wasu hukumomi wanda ya shafi na Fili da gine gine.

Yayin zaman, lauyan mai kara Aliyu Ahmed ya bayyana muhimmancin gama gudanar da hukuncin Karan da akayi.

Jawabin daga hunkuncin kotu daga bakin Justice Amobeda cewa,

“ kotu ta bada umarnin wa wanda ake kara da hukumomi ko Ma’aikatan da Duk wanda suke da hanu ciki da su janye wajen shiga, kai farmaki, ko rusa dukiyar wanda ya kawo kara”

Ya Kuma jaddada muhimmancin kai dokar kotu wa duka jami’un dan bin ka’idar gudanar wa. Kuma kotun zata sake zama ran goma ga watan yuli na shekarar 2023, dan cigaban karar.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button