Man United Zasu Sayi Gola Bayindir Idan Henderson Zai Tafi
Manchester United zasu sayi golan Fenerbahce “Altay Bayindir” akan kudi £4.2m.
Dan wasan “Altay Bayindir” dan kasar Turkey, zaizo Manchester United ne idan gola “Dean Henderson” zai tapi Crystal Palace domin sune a gaba a neman sa bayan Nottingham Forest da suke neman sa a loan.
Ana kan gudanar da bincike akan Bayindir, domin tabbatar da zuwan Man United. Bayan zuwan Bayindir Fernerbahce a 2019, yayi nasarar hana saka kwallo ko daya a ragar sa a wassanni 44 cikin 145 daya kama wa Fernerbahce a gasar da suke ciki gaba daya.
Bayindir shi ne na farko a cikin gololin da Man United suke nema, da kuma golan Benfica “Odysseas Vlachodimos” idan Henderson ya bar Manchester United.