Labaran Yau

Ambaliyar Ruwa Ya Kashe Mutum 10 Ya Kuma Rusa….

Ambaliyar Ruwa Ya Kashe Mutum 10 Ya Kuma Rusa Gine Gine

Akalla mutum 10 ne suka rasa rayukan su tare da rushewar gine gine ciki har da gidaje sama da 200 a babban birnin jihar Katsina da kuma karamar hukumar Bindawa ta jihar, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya mamaye gine-gine da tituna a unguwar.

A cewar mazauna yankunan da hadarin ya auku a cikin birnin Katsina, an fara ruwan sama kamar da bakin kwarya da karfe 4 na yammacin ranar Talata har zuwa daren jiya.

Ungwar Sabuwa da ke kan hanyar Kofar Kaura ita ce unguwar da ruwan saman ya fi shafa a cikin babban birnin Katsina.

Labarin ya zo cewa an ga mazauna unguwar suna kokarin kwashe kayansu daga gine-ginen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su.

Mai Unuwar yankin, Yunusa Rico, ya shaida wa Manema labarai cewa mutane 10 ne suka mutu a bala’in, ciki har da wani jariri, wanda har yanzu ba a ga gawarsa ba.

Ambaliyar Ruwa Ya Kashe Mutum 10 Ya Kuma Rusa Gine Gine
Ambaliyar Ruwa Ya Kashe Mutum 10 Ya Kuma Rusa Gine Gine

A cewar Rico, bala’in ya faru ne sakamakon rashin magudanar ruwa a unguwar da abin ya shafa, saboda babu wata hanyar da ruwan zai wuce daga Kofar Kwaya da Kofar Kaura.

Hakazalika, a karamar hukumar Bindawa, Jaridu sun rawaito cewa akalla gidaje 200 ne suka ruguje sakamakon ambaliyar ruwan sama.

A halin yanzu, Gwamna Dikko Radda a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Ibrahim Mohammed ya fitar, ya ce mutane biyu ne kawai suka mutu a ambaliyar.

Gwamna Radda ya jajanta wa wadanda abin ya shafa da iyalansu, inda ya ce tuni aka fara kokarin shawo kan lamarin da kuma hana afkuwar irin haka nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button