Labaran Yau

Ofishin Yan Sanda Ta Kasa Ta Janye Jami’an Ta Daga Cikin Tsoffin Masu Mukamai

Ofishin Yan Sanda Ta Kasa Ta Janye Jami’an Ta Daga Cikin Tsoffin Masu Mukamai

Babban Ofishin yan sanda ta kasa Abuja, ta fitar da rahoton cewa ta janye jami’an ta daga jikin yan siyasa da wanda suka riqe mukaman gwamnati.

A takarda mai Lamba CB: 4001/DOPS/45PMF/FHQ/ABJ/VOL.15/353 na doka da aiki, tace “Mun janye jami’an mu wanda suke jikin wannan yan siyasan.

“Tsohon gwamnan Jihar Imo Chief Ikedi Ohakim, Tsohon sakataren gwanatin tarayya Boss Mustapha, Tsohon gwamnan Bauchi Adamu Mu’azu, tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje.

Acikin su Akwai “tsohon gwamnan jihar ogun Gbenga Daniel, tsohon gwamnan zamfara matawalle, tsohon ministan lamuran yan sanda Maigari Dingyadi, tsohon ministan jiha ta man fetur Timipre Silva, Tsohon kilakin Majalisan tarayya, Aisha Buhari, dan uwan buhari Alhaji Daura.

“Shugaban mata na jam’iyyar APC, tsohon ministan jiha na mine da steel, Tsohon Ciyaman na kwamitin lamuran yan sanda na Majalisan dattawa Halliru Dauda Jika,  tsohon ministan fasahar science da taknolaji, tsohon ministan jiha kan wutan lantarki.

Akwai “Tsohon shugaban jam’iyyar PDP Sanata Iorchia Ayu, tsohon ciyaman na kwamitin yan sanda Rabiu Lawan, tsohon ministan jiha na kasafi da tsare tsare Prince Clen Ikanade Agba da  tsohon Sanata Stephen Adey”

Takardan tazo da umarni na gaggawa.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button