Farfesa Sulaiman Bogoro ya samu sarautar Jagaban Tapshin
A garin tapshin dake karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar bauchi, sun baiwa tsohon shugaban Tetfund sarautar “Jagaban Tapshin” wa Farfesa Sulaiman Bogoro.
Sarautar tazo ne bisa hazaqar shi wajen kawo cigaba wa kauyuka da Kuma kasa gaba daya cewar Mai gundumar, Dauda Godit.
Anyi bikin sarautar ne hade da bikin su na Al’ada da akeyi kowani mako, bikin ya faru ne a filin Makarantar sakandare da take garin tapshin ran talata.
Mai gundumar ya yabi Bogoro dan aikin Alkhairi da yayi a yankin na shekaru 20 da suka gabata.
Ya kara da cewa, tsohon shugaban tetfund ya bada gudumawa masu yawa tun daga makarantu da kuma kudade dan tallafin karatu.
“Ya kawo cigaba ta fannin ilimi tun Kamin ya zama shugaban tetfund a shekarar 2014” a bayanin sa.
Godit ya yaba wa bogoro matuka wajen inganta Makarantun jami’a a kasa gaba daya zuwa matsayin daya dace a shugabancin sa na tetfund.
Kusan duka jami’un kasar na gwamnati sun samu canji na gine gine da kuma horaswa.
Sun yaba masa ne dan kokarin inganta cigaba na bincike a fanin ilimi wanda ya taimaka Kuma zai taimaka wajen cigaban kasa gaba daya.
Wajen mu’amala, Godit ya yabawa mishi wajen hada kan mutanen Dass, tafawa balewa da Bogoro a mazabar majilasan tarayya.
“Ya dage wajen cigaba Kuma ya kawo cigaba “
Cewar Godit.
A jawabin farfesa Bogoro, ya bayyana cewa sunyi hakan ne dan su kawo zaman lafiya tsakanin addinai a kasar.
“Siyasa na shine in kaci abinci a gidanka Toh ka taimakawa makocin ka in yana bukata, hakan yana nuna kaima kana bukata” a cewar sa.
Bikin Al’adan meh suna Kang khishi Masur 2023, ya samu halartan jama’a da yawa kamar su Farfesa Sylvester shykil (SAN) daga jami’an Jos, dakta Justina deshi da sauransu.
A bikin an gayyaci masu rawan Al’ada daga ciki da wajen kauyen tapshin da kuma yan rawar Zaar.