Labaran YauNEWS

Naso Ace Iyayen Yara Sunsan Alfanun Gwajin Shaye-shaye Wa Mazaje Kafin Basu Aure – Buba Marwa

Naso Ace Iyayen Yara Sunsan Alfanun Gwajin Shaye-shaye Wa Mazaje Kafin Basu Aure – Buba Marwa

Zuwa yanzu, galibin ‘Yan Nijeriya na yin sam-barka da irin yadda Hukumar Hana Fataucin Miyagun Kwayoyi ta NDLEA ke yaki da wannan alkaba’i a kasa. Damke shahararren dansandan nan, DCP Abba Kyari bisa zargin hannu a badakalar hodar ibilis daya ce daga cikin manuniyar yadda hukumar ta dukufa a bisa jagorancin shugabanta, Birgediya-Janar Buba Marwa mai ritaya. Buba Marwa.

Buba Marwa yayi qarin haske gameda yanda tarin matasa ke shiga harkar shaye-shaye dumu-dumu

DOWNLOAD MP3

A baya-bayan nan an samu yawaitar kama masu ta’amuli da safarar miyagun kwayoyi da yawa a Nijeriya, ciki har ma da wani mataimakin kwamishinan ‘yan sanda wanda ake zargi da laifi da suka shafi safarar miyagun kwayoyi.

A halin da Nijeriya take ciki babu wani masifa da ke tare da mu da ta kai masifar shaye-shaye. Saboda ban da lalata matasanmu da wannan masifa take yi. Bincike ya tabbatar da cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi ita ce take ingiza masu aikata muyagun laifuka kamar su garkuwa da mutane, ‘yan bindiga dadi, Boko Haram, barayi, ‘yan fashi da makamantan su. Za mu fahimci hakan idan muka dubi yadda kusan ko da yaushe aka kama su, za ka samu sinkin miyagun kwayoyi a tare da su tamkar shi ne kadai abincinsu.

A cikin jawabinshi Buba marwa yabada shawara wa iyaye dasu ringa taka tsantsan wajen aurar da yaransu, saboda gujewa haduwa da miji dan shaye-shaye, inda yace idan ta kama har gwaji suna kaisu hukumar NDLEA don gwaji.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button