Subhanallahi Adam A. Zango ya saki matar sa saboda ta saka hoton ta a shafin TikTok Jarumi Adam A Zango ya saki matar sa Safiya Chalawa sakamakon saka hoton ta a manhajar TikTok.
Jami’inmu na Labaranyau Blog ya samo rahoto cewa jarimin ya bayyana hakan ne a wani video a shafin sa na TikTok.
A cewar Zango, sai da ya gargade ta tun farkon auren su akan saka hotuna a social media.
Sannan ya bayyana cewa ya gargade ta akan wata sana’a da yace tana yi a gidan sa amma bata daina yi ba.