NEWSLabaran YauPolitics

Maiyin Tattaki Don Ganin Tinubu Ya Isa Ibadan

Maiyin Tattaki Don Ganin Tinubu Ya Isa Ibadan

Bakanon da ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas domin nuna goyon bayansa ga takarar Sanata Bola Tinubu, Husseini Lawal, ya isa Ibadan babban birnin Jihar Oyo.

Mutumin dan asalin Kano ya fara tattaki ne zuwa Legas tun bayan da Tinubu ya ayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar nan a kakar zabe ta shekarar 2023.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Dadin dadawa ya shaida wa manema labarai cewa ya fara tattakin ne domin nuna goyon bayansa ga tsohon Gwamnan Legas saboda ya ce shi kadai ne dan takarar da ya damu da matasa a cikin masu neman takarar shugabancin a shekarar 2023.

“Tinubu ya na goyon bayan matasa tun kafin ya zama Gwamna a Legas; haka kuma lokacin da yake Gwamnan da ma bayan ya bar kujerar. Don haka nake kira ga ’yan Nijeriya da su mara wa Tinubun baya a zabe mai zuwa.” Inji mai tattakin.

Hussein ya isa birnin Ibadan a daren shekaranjiya Litinin inda ya bayyana cewa yayin tattakin nasa yana samun tallafi na kudi da sauran abubuwa daga sojoji da direbobin da yake haduwa da su a kan hanya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button