Labaran YauNEWS

Zakaci Zabenka Idan Kadaukeni Mataimaki- Sakon Rochas Ga Tinubu

Zakaci Zabenka Idan Kadaukeni Mataimaki- Sakon Rochas Ga Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma Sanata mai wakiltar Imo ta yamma a majalisar dokokin kasar,  Sen Rochas Okorocha, ya bayyana aniyarsa ta hada kai da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a takarar shugaban kasa a 2023 a matsayin mataimakinsa.

Mista Rochas Okorocha ya ce idan har ya yi wu a basu tikitin takara, Tinubu da Rochas a zaben shugaban kasa na 2023, to lalle za suyi nasara ba nakawa.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwa kan yuwuwar su lashe zaben, inda ya bayyana cewa mutane suna kaunarsu ne saboda suna tausaya wa bil’adama da kuma gujewa kabilanci.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban taron jam’iyyar APC na kasa da aka kammala a Abuja ranar Asabar.

Ya ce, “Ni da kawu Tinubu mun fi dacewa. Na yi imanin cewa in lokacin yayi lamarin zai wakana, Tinubu shi ne jagaban Kudu maso Yamma, kamar yadda nake a Kudu-maso-Gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button