Labaran Yau

Mutum 8 Da Kan Iya Fitowa A Sunayen Ministocin Tinubu

Mutum 8 Da Kan Iya Fitowa A Sunayen Ministocin Tinubu

Dai dai lokacin da hasashe na mutane daban daban ke ta zagayawa kan su wa shugaba Tinubu ke shirin bayyanawa a matsayin ministocinsa, alamu na nuni da cewa wasu ‘yan siyasa da suka yi gwamna da ministoci za a iya sake yin amfani da su cikin majalisar ministocin na Tinubu, duk kuwa da korafe-korafen da wasu ‘yan Najeriya ke yi na sake amfani da ‘yan siyasa.

Yayin da da yawa na iya yin korafi a kan wadannan ‘yan siyasar da ake ganin sun ci gaba da kasancewa a kowace gwamnati mai ci, har yanzu ana iya bukatar kwarewarsu ta shugabanci.

Wasu daga cikin ‘yan siyasa a wannan fanni sune:

1. BABATUNDE FASHOLA

Babatunde Fashiola
Babatunde Fashiola

Babatunde Fashola Fashola ya kasance amintaccen aminin shugaba Tinubu tun zamanin da yake gwamnan jihar Legas. Fashola ya yi minista ne a karo na biyu a lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon ministan ya gaji Tinubu a matsayin gwamnan jihar Legas kuma yana iya zama minista a sabuwar gwamnatin ta Tinubu.

2. NASIR AHMED EL`RUFAI

El Rufai
El Rufai

Nasir El-Rufai tsohon gwamnan jihar Kaduna ya taba rike mukamin ministan babban birnin tarayya a karkashin gwamnatin Olusegun Obasanjo tsakanin 2003 zuwa 2007.

Akwai yiwuwar El-Rufai ya dawo a matsayin minista karkashin gwamnatin Tinubu, duba da irin gudunmawar da ya bayar. don samun nasarar jam’iyyar APC da kuma shugaba Tinubu a zaben 2023, musamman ma lokacin da aka bullo da sabbin takardun naira a lokacin yakin neman zabe.

3. NYESOM WIKE

 Nyesom Wike
Nyesom Wike

Nyesom Wike Tsohon gwamnan jihar Ribas ya taba zama karamin ministan ilimi a watan Yulin 2011 kuma ya samu mukamin ministan ilimi a lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Wike ya sauka ne domin ya tsaya takarar gwamnan jihar Ribas a shekarar 2015. Ya lashe zaben kuma ya yi wa’adi na biyu.

Tsohon gwamnan na iya komawa mukamin minista a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, duk da cewa ya yi shekaru da dama a karkashin jam’iyyar.

4. KAYODE FAYEMI

Kayode Fayemi
Kayode Fayemi

Kayode Fayemi Fayemi ya taba rike mukamin ministan bunkasa ma’adanai a karkashin tsohon shugaban kasa Buhari daga watan Nuwamba 2015 zuwa Mayu 2018 lokacin da ya yi murabus ya tsaya takarar gwamnan jihar Ekiti kuma ya yi nasara.

5. RABI`U KWANKWASO

Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso

Rabiu Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya bayyana cewa yana neman kujerar minista tare da tsohon gwamna kuma wanda zai gaje shi, Abdullahi Ganduje.

Kwankwaso dai ya kasance ministan tsaro a gwamnatin Obasanjo kuma ya fito fili ya bayyana fatansa na yin aiki da gwamnatin Tinubu.

Jim kadan bayan rantsar da shi, rahotanni sun ce Tinubu ya gana da Kwankwaso a kasar Faransa, al’amarin da ya kusa kayar da shi da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, musamman na Arewa.

5. ATIKU BAGUDU

Rabiu Bagudu
Rabiu Bagudu

Atiku bagudu wanda yake tsohon gwamnan jihar Kebbi shima ya taka rawar gani a tafiyar siyasar APC kuma ya kasance jigo a yakin neman zaben Tinubu watannin da suka gabata, kuma Bagudu din shine wanda ya rike mukamin shugaban karbar Mulki na tinubu daga hannun tsohuwar gwamnati ta Buhari.

6. ABUBAKAR BADARU

Abubakar Badaru
Abubakar Badaru

Abubakar Badaru shima tsohon gwamna ne na jihar Jigawa a arewacin Najeriya kuma shima jigo a yakin neman zaben shugaba Tinubu wanda kuma shima ya shiga cikin tawagar shugaba Tinubu da ta ziyarci kasar Guinea Bissau a yan kwanakinnan wanda a tafiyar ne ma shugaba Tinubu ya samun kujerar zama Jagoran kungiyar Ecowas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button