![ECOWAS Ta Bukaci Goyon Bayan Amurka Da Faransa Akan Al`amarin Niger](https://labaranyau.com/wp-content/uploads/2023/08/imgonline-com-ua-twotoone-TL3YtqpFtAJj.jpg)
Gwamnatin tarayya da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS sun bukaci goyon bayan kasashen duniya domin maido da mulkin demokradiyya a Jamhuriyar Nijar.
Amb. Ibrahim Lamuwa, babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da jami’an diflomasiyya kan halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar a ranar Juma’a a Abuja.
Lamuwa ya ce FG da ECOWAS sun yabawa kasashen duniya da suka yi Allah wadai da juyin mulkin da Janar Abdourahamane Tchiani ya jagoranta wanda ya hambarar da zababben shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum daga mukaminsa a ranar 26 ga watan Yuli.
Hakan kuma na zuwa ne yayin da suke nuna damuwarsu kan lafiyar Bazoum da aka ce gwamnatin soja ta tsare.
“Saboda haka, Najeriya da kuma ECOWAS, suna kira ga kasashen duniya da su jajirce kan wannan matsaya, su kuma ci gaba da nuna goyon baya ga ECOWAS wajen tabbatar da fifikon mulkin dimokradiyya da tsarin mulki a kan mulkin kama-karya.