Jirgin saman Ethiopia babban mai hanun jari na Jirgin
Mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu buhari kan sadarwa na zamani Bashi Ahmad, Yace jirgin saman Ethiopia sune masu mafi yawan hannun jari na jirgin saman Najeriya.
Ahmad yace yan Najeriya su jira dan zasu ga jiragen Ethiopia a jiragen Najeriya wato Nigerian Air.
Tun da labarin jiragen Najeriya ta iso kasar, maganganu ya zaga cewar an karbo hayan jiragen kasar Ethiopia ne.
Ministan jiragen sama Hadi sirika, Ana zargin sa da amfani da jirgin saman Najeriya dan ya saci kudade.
Don korin wannan zargin, Ahmad ya bayyana a shafin tweeter cewa “ba abu ne a boye ba ko sirri cewar jiragen Ethiopia sune masu hannun jari kan jiragen Najeriya. Ku daina Koke koke dan jiragen Ethiopia Suna dauke Kalan kasar Najeriya.
“Kamar jiragen Najeriya, mafi yawan jiragen duniya ba na gwamnatin su bane. Jiragen burtaniya jirage ne na IAG a misali.
“Labarin na watan fabrailu ce, bayan duba da nagari, gwamnatin Najeriya ta zabi jiragen Ethiopia saboda sun samu cigaba ta fannin jiragen sama a nahiyar afrika. Kuma hadin kan jiragen kasar Najeriya da Ethiopia ta bada Ethiopia mallakar jiragen na Kaso 49 cikin dari.
“Gwamnatin Najeriya Tana da kaso biyar cikin dari yayinda yan Najeriya masu hanun jari ke da kaso 46 cikin dari na jiragen Najeriya.
“Burin mu shine jiragen kasar Ethiopia zata kasance Mai Samar da gudanar wa Mai inganci da Kuma jami’ai masana dan aikin jiragen da Kuma bada jiragen su wanda zata dauki kalar kasar Najeriya”