EntertainmentLabaran Yau

Hausawa Kudaina Haihuwa Barkatai- Nafisa Abdullahi

Hausawa Kudaina Haihuwa Barkatai- Nafisa Abdullahi

Fitacciyar tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta yi kira ga masu haihuwar iyalai barkatai ba tare da kula da su ba da su guji yin haka.

Ta bayyana haka ne a wasu sakonni da ta wallafa a shafinta na sada zumunta Tuwita ranar Asabar.

DOWNLOAD MP3

Ku daina haihuwar ‘ya’yan da kuka san ba ku da halin kula da su,” in ji Nafisa.

Ta kara da cewa Allah zai tuhumi mutanen da suke haifar ‘ya’ya ba tare da sauke nauyin da ya dora musu ba.

A cewarta: “Kun ga dukkan mutanen da ke haifar ‘ya’yan da ba su ji ba ba su gani ba, domin kawai su aika da su almajiranci, kuma su ci gaba da haifar karin ‘ya’ya, Allah sai ya saka wa yaran nan!!!”

DOWNLOAD ZIP

Ta bayyana matukar bacin ranta kan yadda wasu iyaye suke tura ‘ya’yansu ‘yan shekara biyu zuwa uku almajirci.

Tauraruwar ba ta ambaci sunayen wadanda take yi wa wannan gargadi ba, sai dai dama ba sabon abu ba ne yadda a kasar Hausa ake tura kananan yara almajirci.

Wannan lamari ya dade yana bata wa mutane da dama rai, musamman ganin cewa wasu na zargi ana amfani da irin wadannan yara wajen aikata laifuka.

Sai dai kalaman tauraruwar sun jawo martani daban-daban inda wasu suke yaba mata yayin da wasu suke sukar ta.

Ko ya kuke ganin wannan batu na Nafisa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button