Labaran Yau

Jirgin Sama Na Air Peace Sun Bayyana Zasu Dawo Da Yan…

Sudan: Jirgin sama na Air Peace sun bayyana zasu dawo da yan Najeriya kyauta

Air peace, Jirgin sama na kasuwa a Najeriya, sun bayyana shirin su na taimakawa yan Najeriya dan dawowa dasu daga Sudan, wanda keh yankin arewa ta gabas dake nahiyar Afrika kyauta in gwamnatin tarayya zata iya sama musu filin jirgin a kasashen dake makwabta da kasar.

Shugaban kampanin Allen Onyema, ya bayyana hakan a bayanin da yayi ran litinin.

Onyema ya ce hakan yazama dole dan yan Najeriya barasu rasa rayukansu a kasar ta Sudan ba. A kokarinsa dan ya taimaka wa yan Najeriya dan basu san yanda zasu yi ba cikin hali na yaki.

“Air peace tayi niyan fitar da yan Najeriya da suka tsinci kansu a halin yaki a kasar sudan kyauta, in har gwamnati zata iya kaisu inda zasu samu filin jirgin sama Koh da kasashen dake makwabta da kasar. Ba komai ne za a barwa gwamnati tayi ita kadai ba.

“Mun shirya muyi yanzu yanzu, babu bata lokaci, Duk abinda zai kawo kare kiman Najeriya, hadakaiya da zaman lafiya shine a gaban mu.

“ Bamu da nasani dan yarda da kasar mu Kuma Muna kaunar kasarmu Duk da matsalolin da ake fuskanta. In an kai su Uganda koh kenya koh wata kasa, Zamu shiga dan fitar dasu. Wasu daga cikin iyaye Suna kiran mu dan mu taimaka, Muna shirye dan mu taimaka Kuma zamu Kuma” a cewar sa

DailyNigeria ta rawaito Labaranyau ta fassara

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button