Labaran Yau

Jirgi Mai Rubuce Da Nigeria Air Ta Haya Ne Daga Ethiopia

Jirgi Mai Rubuce Da Nigeria Air Ta Haya Ne Daga Ethiopia

Kaptin Dapo Olumide, mai rikon kwaryar manajan darakta na Nigeria Air, Yace jirgin da ta shigo kasar da logon Najeriya wanda shatan ta akayi a jiragen Ethiopia dan a nuna logon.

Olumide, ya fadi hakan ranan talata a Abuja, bayan ya ziyarci gayyatan kwamitin majalisan dattawa akan safaran sama.

Yace jiragen saman har zuwa yanzu lasisi bai samu ba wajen gudanarwan aikin. Yace lamuran an fara su kenan.

Mista Olumide yace aikin shi shine ya samo lasisin gudanar da jiragen sama ba dan kuma ayi aiki dasu ba.

“Jirgin da ta shigo ta fita anyi shatan ta ne ta hanya Mai kyau. In zakayi biki zuwa senegal zaka iya daukan shatan jirgi.”

“Baka bukatan lasisi, zakayi shatan jirgi ne, in ka biya kudin jirgi, jirgi zaizo ne ya diba mutane ya tafi.

“Abinda mukayi kenan amma dan mu nuna logon Najeriya.

“Tun shekarar 2018, Duk abinda kaji akan jiragen Najeriya a hoto ne ko Zane. Mun nuna wa masu saka hannun jari ne su gani dan su gane yanda jiragen zasu kasance.

“Akwai masu saka hannun jari Na shekara goma zuwa sha biyar, Suna bukatan ganin yanayin jiragen.

“Mun shigo dashi mu nuna yanda zai kasance Sai Kuma shafin Sada zumunta suka mayar dashi wani abu daban.

“Kamin mu samu lasisin wanda aiki na ne, Sai mun samu jirage guda uku, kamin NCAA su bamu lasisi, Kuma Sai jiragen sun samu rajistan Najeriya.

“Bayan jirgin da mukayi shata ta iso, akwai mutane masu ilimi wanda yakamata suyi bayani wa mutane amma kuma sunki suyi”

Ciyaman din kwamitin ya ce tsohon ministan yayi rashin azanci na saka stakeholders a cikin aikin Jiragen Air Nigeria.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button