Labaran Yau

Gwamnatin Tarayya Ta Amince A Fitar Da Kudi Dala Miliyan 1.2 Dan Ceto Yan..

Sudan: Gwamnatin tarayya ta amince a fitar da kudi dala miliyan 1.2 dan fitar da yan Najeriya

Ministan kula da Al’amuran waje, Goeffrey Onyeama, ya bayyana sakamakon zaman da sukayi wa manema labarai, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman ranan laraba a Birnin tarayya Abuja.

A cewar Onyema, kudaden za kashe su ne wajen hayan manyan mototi dan safaran yan Najeriya a Sudan zuwa Kasar masar inda jirgi zata kashesu zuwa Najeriya.

Yace, “Saboda bada bayani kan abinda ke faruwa game da fitar da yan Najeriya a Sudan.

DOWNLOAD ZIP/MP3

“In ba manta ba kalubale da aka samu shine na Yardan gwamnatin Sudan da jami’an tsaro dan kula da fitan yan Najeriya.

“Saboda munyi shawaran safaran yan Najeriya zuwa bodan kasar masar, Aswan.

“Muna aiki da embassy ta Najeriya a sudan dan aiwatar da aikin fitar da yan Najeriya wanda Mun fara Kuma Muna jin dadin haka.

“Dala miliyan 1.2 aka caje mu na mototi 40. Muna da manya manyan mototin bus wanda aka tanadar wa yan Najeriya zuwa bodan masar.

“Saboda kalubale dake tattare a ciki, mutane dayawa na so suyi amfani da daman dan cimma burinsu.

“Mun ga abinda ya faru na harin da aka kai wa ayarin motocin faransa. But a hakan zamuyi dan rayukan yan Najeriya shine mafi amfani a gare mu”.

Karamin ministan waje Zubairu Dada, ya bayyana cewa babu dan Najeriya ko guda daya rasa ranshi a wannan yakin na Sudan.

“Ina tunanin abinda yafi muhimmanci shine a yan Najeriya su dawo cikin koshin lafiya Kuma Muna fatan baramu rasa ran koh mutum daya ba, In shaa Allah. Komai na tafiya daidai kuma baramu samu matsala ba.

Dada ya jaddada cewa gwamnati Tana iya bakin kokarin ta wajen hado kan jami’an tsaro da kuma fitar da yan Najeriya zuwa bodan masar.

Ya ce, gwamnati Tana kokari ta fidda su a cikin awanni 72 wanda gwamnatin sudan ta bada dan fita.

Bamu damu da awa 72 da aka bamu ba saboda duka jami’an da muke magana dasu Suna aiki ne a yanda muka tsara.

“Magana akan kofar da Sudan tabayar, Muna kokari muga munyi amfani dasu dan fitar da yan Najeriya dayawa”

Ya ce wasu yan Najeriyan sun samu fita ta ruwa wanda gwamnatin Saudi Arabia ta dau nauyi.

“Wasu yan Najeriya sun samu taimakon abokai kasashen duniya, wanda Saudi ta dau nauyin fitar dasu a jirgin ruwa zuwa Jeddah. Daga nan Zamu muyi kokarin dawowa dasu zuwa Najeriya”.

Sakamakon zaman da akayi, ministan noma, Mohammed Abubakar, gwamnati ta yarda a Gina babban ofishin da kudi biliyan 6 na ofishin ministirin noma.

Yace ofishin za a gina mai hawa goma Kuma za a sa mai suna gidan noma(Agriculture House).

Ministan Yace tun dawowa a Abuja, babu babban ofishin ministirin noma.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button