Labaran YauNEWS

Ni Ne Daidai Da Yen Ta’addan Nijeriya-Atiku Abubakar

Ni Ne Daidai Da Yen Ta’addan Nijeriya-Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar ya ce idan ‘yan Nijeriya suka zabe shi 2023 a matsayin shugaban kasa zai tabbatar da cewa babu wani dan ta’addan da zai samu iskar shakar da har zai kaddamar da ta’addanci akan al’ummar Nijeriya.

Alhaji Atiku Abubakar ya fadi haka ne a lokacin da ya kai wata ziyara cikin jihar Katsina dake fama da hare haren yan ta’addan daji masu garkuwa da mutane.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar neman mulkin Nijeriya, Atiku Abubakar, ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar nan, Yan Ta’addan Daji Masu Garkuwa Da Mutane bazasu Kara samun sakewa ba.

Atiku Abubakar ya furta wannan kalaman ne a ya yin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP a cikin jihar Katsina, Atiku Abubakar ya ce sakacin shugabanni ne ya ba yan ta’addan Nijeriya damar ci gaba da shakar iska a cikin Kasar nan.

Atiku Abubakar ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben shekarar 2023 zai tabbatar da cewa babu wani dan ta’addan da zai kara tayar da ta’addanci a kan yan Nijeriya.

Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa Alhaji Atiku Abubakar ya ce yana mai tabbatar ma da al’ummar Nijeriya cewa idan suka bashi hadin kai ta fuskar goyon bayan shi a zaben 2023 shi kuma zai mayar da kai fannin tsaro wanda zai sa matsalar ta zamo tarihi a cikin Nijeriya baki daya.

Alhaji Atiku Abubakar ya ce tabbas zaman lafiya shine babban jigo a cikin kowace kasa kuma zayyi iyakacin kokarin shi domin ganin Nijeriya da yan Nijeriya sun zauna lafiya idan ya yi nasarar zama magajin shugaba Buhari.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button