Ranar Masoya Ta Dunìya Rana Cé Waccé Ta Samó Asali Daga Labarín Sóyayya Wanda Ya Farú A Gaské
Yau neh ranar Masoya na duniya, jami’inmu na Labaranyau Blog yayi kokarin kawo mana cikakken tarihin ranar soyayya wanda Bashir Abdullahi El-bash ya wallafa a shafinsa
Ranar 14 Ga Watan Fefruware Na Kowaccé Shekara, Rana Ce Ta Masoya Wacce Ta Samo Asali Daga Labarin Soyayyar (Valentiné) Wanda Aka Kashé Shi Saboda Soyayya A Daular Romawa.
Yau Talata, 14 Ga Watan Februware 2023.
Ranar masoya da mu ka sani wacce ake raya ta ta hanyar aikewa da saƙonni da kyaututtukan soyayya a tsakanin masoya, labari ne na gaskiya mai cike da darasi wanda ya ke nuna tsantsar ƙauna da soyayya matuƙa da kuma sadaukarwa kan soyayya ta gaskiya da gaskiya, mai cike da bayanin haƙiƙanin ranar masoya.
Tarihí ya labarta céwa a cikin ƙarni na uku, an yi wani sarki mai suna Sarki Claudius II Gothicus a Daular Romawa wanda ya gawurta wajen zaluci da tsanani wajen gudanar da mulkinsa. Saboda tsananin zaluncisa ne ma aka yi masa laƙabi da suna Mugu (Cruel).
Ya kasance sarki mai yawan takalo yaƙi da kuma tauyewa al’ummarsa haƙƙoƙinsu. Ya kuma fafata a yaƙoƙi da dama a wannan ƙarni na uku. Ba tare da wadatattun rundunar mayaƙa ba.
Sarki Cladius ya yi imani cewa za a cigaba da ɗíban sojoji dan haka ne ma ya haramta duk wani aure da harkokin soyayya da masoya a wannan Daula ta Romawa.
Saboda acewarsa mazan ronawa su na girmama soyayya ba sa son fita su bar masoyansu. Ɗaruruwan masoya da su ke fata da son zama ma’aurata sai haƙura su ka yi da cika burukansu saboda zaluncin wannan sarki wanda babu wanda ya isa ya ɗaga masa murya kan duk wani ƙudiri da ya zartar.
Sai dai an samu wani shugaba a cikin addinin kirista mai suna Valentine wanda ya bijirewa wannan umarni na wannan sarki, inda ya fara yin soyayya a ɓoye da aure a cikin sojojí kafin su fita filin yaƙi.
A shekarar 269 Sarki Claudius ya gano wannan ɓoyayyen sirri na bukukuwa da ake shiryawa a ɓoye inda ya kama Valantine ya ɗaure shi a gidan kurkuku tare da zartar masa hukuncin kisa.
A zaman Valentine a gidan kaso ya na zaman jiran a zartar masa da hukunci kisa, ya fara soyayya da wata makahuwar budurwa a gidan kaso inda ya rubuta mata waken soyayya wanda kuma hakan ya yi sanadiyyar dawo mata da ganinta. A daidai lokacin da ya rage kwana ɗaya a kashe shi.
Ya sadaukar da rayuwarsa saboda soyayya an kuma kashe shi akan soyayya.
Bayan wannan ne kuma cocin Katolika ta ware ranar 14 ga watan Fefruware a matsayin ranar masoya domin a riƙa tunawa da kuma girmamawa Valentine wanda ya sadaukar da rayuwarsa akan soyayya. Inda masoya ke aikewa junansu kyaututtuka da saƙonnin soyayya a wannan rana.
A duk duniya masoya su na tunawa da wannan rana su na kuma girmamata. Soyayya ta gaskiya ta na buƙatar sadaukarwa da juriya da kuma jajircewa kanƙaunar juna da nunawa juna soyayya ta hanyar faɗawa juna kyawawan kalaman soyayya da kuma sadaukar da ranakun hutu ga soyayya domin zama da juna da tattaunawa da ƙara ƙarfafa so da ƙauna a tsakanin masoya.
Kulawa ita ce ajin farko da ke ƙara bayyana ƙarfin soyayya da kuma ƙara kyautata dangantakar da ke tskanin masoya.
Stream bidiyon valentine