Alamu masu karfi na nuni cewa karin hare-hare ta sama da rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ke yi a ‘yan kwanakin nan na iya tilastawa jagororin ‘yan ta’adda a jihohin Katsina da Zamfara yin tunanin barin makamansu domin shiga fagen tattaunawa da gwamnatin tarayya.
Sakamakon yadda aman wutar ta hargitsa su, an yi imanin matakin na nuni da wani abu na tsoro da firgita daga bangaren ‘yan ta’addan da suka yi zargin cewa hare-haren bama-bamai ta jiragen sama na ci gaba da kai wa rayuwarsu da gidajensu da dabbobinsu hari.
Wata majiya mai tushe da ta bayyana kokensu ta bayyana cewa, a ranar 15 ga watan Yulin 2023, Sarkin ‘yan ta’addan da ke Katsina, Usman Kachallah, ya gana da ‘yan ta’addansa a wani wuri kusa da kauyen Gusami a karamar hukumar Birnin Magaji (LGA) domin tattauna halin da suka samu kansu.
Shugabannin ‘yan ta’addan da ake zargin sun gana da Kachalla domin neman hanyoyin tunkarar Gwamnati domin ganin an shawo kan matsalar tsaro da suka hada da Abdullahi Danda, Alhaji Shingi da Lauwali Dumbulu da dai sauransu.