Labaran Yau

Mason Mount Ya Kafa Babban Tarihi A Manchester United

Mason Mount Ya kafa tarihi a Manchester United

Biyo bayan sanarwar Kammala daukan Dan wasan da kungiyar ta Manchester United tayi a jiya da safe akan dala miliyan Hamsin da biyar, Dan wasan wanda haifaffen kasar ingila ne ya shiga jerin yan ingila Wanda suka saka riga wai dauke da namba bakwai a bayansu.

David Beckham shine Dan wasan ingila a baya bayan nan daya goya wannan namba mai cike da tarihi. Magoya bayan kungiyar suna matukar girmama wannan namba duba da wadanda suka saka ta a baya Wanda sun hada da tsohon Dan kwallan kafar faransa wata Eric Cantona da kuma shahararren Dan kwallon kafar kasar Portugal wato Cristiano Ronaldo.

Sauran da suka saka wannan lamba sun hada da Michael Owen, Antonio Valencia, Memphis Depay da kuma angel di Maria.

DOWNLOAD MP3

Jim kadan bayan rattaba hannu a kan takardar kwantaragin sa na shekara biyar ya shaidawa manema labarai cewa

Mason Mount
Mason Mount

“yana matukar farin cikin taka leda a karkashin kocin kungiyar wato Erik ten haag” Ya kara da cewa “ba abu bane mai sauki na barin tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea amma lokaci yayi na fuskantar wani kalubalen a rayuwarsa a matsayin dan kwallo”.

Daga karshe kuma, kocin Manchester United din ya shaida masa cewa, “inaso ka zama daya daga cikin yan kwallonmu masu bada babbar gudunmawa a kakar wasanni mai zuwa.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button