Labaran Yau

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Rage Kwanakin Aiki Zuwa Uku Saboda Tsadar Abun Hawa

Gwamnatin Jihar kwara ta rage kwanakin aiki zuwa Uku saboda tsadar abun hawa

Gwamnatin jihar kwara ran litinin ta bada umurni na rage kwanakin zuwa aiki, daga kwana biyar zuwa uku a cikin sati a Jihar.

Gwamnatin tayi hakan ne bisa tashin farashin man fetur wanda ya haddasa karin kudin abun hawa dan zirga zirgan jama’a zuwa wuraren aiki.

A cikin bayanin da ya fito a garin Illorin daga bakin babban sakataren labarai na gwamna Abdulrahman Abdulrazak.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Shugaban ayyuka na jiha, Mrs Susan Oluwole ta bada umurni wa duka ministirin da sauran hukumomi da su sawwaka wa ma’aikata dake karkashin su dan yin aiki na uku cikin sati.

Oluwole Tace gwamnatin ta dau matakin ne dan sauwaka wa mutane da suka tsinci kansu cikin wannan hali na wahala saboda tashin man fetur.

Tace hakan babban mataki ne da suka dauka yayin suka duba yanayi da mutane suka shiga ciki na takuri saboda cire tallafi da gwamnatin tarayya tayi na man fetur.

Ta kara da jaddada cewa mutane kar suyi amfani da wannan daman wajen raina gwamnati ko gwamna, shi yasa ta dau matakin lura da ma’aikata wajen zuwa aiki wanda aikin duban a ofishin ya yake.

Daily trust ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button