Labaran Yau

Kasar Saudiyya Ta Bada Kyautan Dabino Ton Hamsin Wa Najeriya

Kasar Saudiyya Ta bada kyautan Dabino ton hamsin wa Najeriya

Masauratar Saudiyya ranan talata, sunyi wa Najeriya kyautan dabino Mai inganci ton hamsin dan karfafa abota da mu’amala a tsakanin kasashen.

Ambasadan saudiyya a Najeriya Faisal Alghamdi, ya bada wannan kyauta a wata taro da akayi Abuja.

Nezat Talaqi, jagoran taimako na saudiyya KSRelief, Yace kyautan ya fito ne daga masu gudanarwa na masallatai biyu masu tsarki na Sarki Salman Al Saud.

Yace gwamnati saudiyya karkashin Hukumar jin kai ta KSRelief, ta yi kyauta daban daban a fanni daban daban wa Najeriya.

Kuma sunyi kyauta ta karshe wanda ta gabata Kamin wannan, wanda suka Yi kyauta ta abinci ta a jihohi kamar Kano, yobe da borno karkashin kungiyar Et’am wa mutum 48,300, a kalla dalla 500,000.

Jawabin da ya fito daga ofishin saudiyya ta Najeriya ta bayyana cewa zasu Kuma bada taimako a fannin lafiya a Abuja, Kano da legas wanda za a fara kamin karshen shekarar 2023.
Dan taimakawa wa kasashe da Kuma kudirin ta na jin kai ta samu cika ta maikawa wanda suke wahala da rashin kwanciyar hankali.

“Zamuyi kyautan jin kan ne kyauta ba Sai an biya ba wa yan Najeriya.”

Tun bude wannan Hukumar bada tallafi da jin kai a watan mayu shekarar 2015 da taimakon kasashe 175 na Majalisan dinkin duniya, KSRELIEF ta bada kyauta na a kalla dala biliyan 6.2 wa kasashe 91.

Wanda ya amshi kyautan, Janet Olisa, darakta daga ministrin kasa da kasa, ta nuna godiya wa gwamnatin saudiyya, ta ce Najeriya tana godiya da wannan kyautatawa.

Ta bayyana cewa kasashen guda biyu sun jima suna kulle ta alaqa Mai karfi wanda hada kyaututtuka tsakani duk da Suna tare a OPEC dalilin mai, amma kuma Najeriya tana godiya da tsaya wa yan kasa dan aikin hajji.

Kuma dabino za a bada ministirin jin kai su raba wa yan Najeriya yanda zai sanya kyautan a zukatansu.

Daily Nigeria ta rawaito

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button