Labaran Yau

Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sake Tsohon Mataimakin Gwamnan Jahar Nassarawa Daga Hanun..

Yan sanda sun tabbatar da sake tsohon Mataimakin gwamnan jihar Nasarawa daga hanun yan garkuwa

Farfesa Onje Gye-Wado, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Nasarawa ya samu tsira daga hannun yan garkuwa wanda suka yi awun gaba dashi ran 7 ga watan Aprailu.

DSP Ramhan Nansel, Jami’i wanda ya kasance mai lura da sanar da jama’a ya bayyana wa hukumar labarai ta Najeriya cewa ranan Monday a lafiya.

Shi mataimakin gwamna ne a karkashin Mulkin ABDULLAHI Adamu daga shekarar 1999 zuwa 2003, Masu garkuwa sun dauke shi ne a gidansa dake karamar hukumar wamba.

DOWNLOAD MP3

Jami’in yan sandan ya bayyana cewa farfesa ya samu dawowa gida da misalin karfe taran dare ranan lahadi. Kuma yana tare da iyalinsa.

Nansel ya kara da cewa har a yanzu basu kama kowa ba kan garkuwa da akayi da Farfesa. Kuma yan sanda basu masaniya koh anbiya kudi wajen sake shi ba.

Yace an sake dattijon ne sabida takurin da yan sanda sukayi wa masu garkuwan.
Dailynigeria ne ta rawaito.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button