Gwamnan Gombe yayi bakin cikin rashin wazirin Cham
A jawabin darakta janar Na zantarwa na gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya yayi bakin cikin rasuwan wazirin Cham, Baba KK Cham, wanda ya rasu ran 8 ga Aprailu a shekaran 2023, bayan dogon jinya da yayi.
A wasikar ta’aziyyar da gwamna Muhammad Yahaya Inuwa ya bayyana cewa shi marigayi Nagartacce mutum ne kuma mai fada a ji, shugabane wanda dabi’un sa abun koyone.
Ya kara da cewa ya tuna yanda waziri ya kasance daban da mutane dayawa wajen aiki matuka a Duk inda yayi aiki daga ministri, da sashe sashe zuwa hukumomi wanda ya kawo cigaba a kowani fanni a jihar gombe.
Gwamnan ya mika ta’aziyar sa cikin bakin ciki ga iyali da mutan garin Nidu-gra Cham da cham gabadaya na wannan rashi da akayi.
Marigayi Wazirin Cham ya kasance tsohon ma’aikacin gwamnati, ya aiki a wurare dayawa, tundaga gwamnatin yankin Arewa ta gabas, tsohuwar jihar bauchi wanda yayi ritaya a matsayin maitaimakin darakta.
Kuma gwamnati ta zabeshi a matsayin mamba kakakin hukumar Alhazai na kiristoci, hukumar asusun gida na jihar gombe da kuma hukumar watsa labarai na gombe da sauransu.