Labaran Yau

Da Dumi Dumi: Yara 17 Suka Rasa Ransu Bayan Karyewar Kwale Kwale A..

Dumi Dumi: Yara 17 suka rasa ransu bayan kwale kwale ta karye a sokoto

A kalla yara sha bakwai maza da mata sun mutu cikin kwale kwalen da ta karye yayin da suke tafiya a ruwan dandeji a karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.

Aliyu dantani, ya kasance chairman wanda ya bayyana hakan wa Hukumar labarai ta kasa a sokoton Najeriya.

Yace hatsarin ya faru ne ranan talata da safe, Kuma gawakin ancire an musu sallah, aka binne su yadda addini ya tsara da misalin karfe biyu da rabi na rana.

Shi chairman din ya bayyana cewa maza da mata a kalla mutum 40 sun tafi nemo icce a dajin da ke kusa dasu, Sai kwale kwalen ta karye.

Yace wasu fasonjojin sun fita da kansu neman tsira, sauran Kuma Ana kan bincikensu a ruwan.

Ma zaunin dajin ya bayyana cewa an samu labarin hatsarin daga bakin Mai kwale kwalen, ya kara da cewa gawawwaki sha bakwai aka fitar, masu sunta sun shiga ruwan Suna kan neman sauran.

Hukumar labarai ta kasa ta bayyana cewa hakan ya taba faruwa ran 13 ga watan Aprailu na shekarar da ta gabata. A wani kauye mai suna Gidan magana, a inda mutum ashirin da tara suka rasa rayukan su wanda mafi yawa matasa ne.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button