Elder Karofi yabada labarin gamuwarsa da wata yarinya tareda mahaifinta a cikin jirgin Azman wanda zata tashi daga Legas zuwa Kano
Akwai wani mutum da na taba haduwa dashi a Jirgi daga Legas zuwa Kano. Farin tsoho ne da farin gashi. Kuma irin masu yawan Tasbihin nan.
Tun muna Murtala Muhammad International Airport yake ta Tasbihi, saboda mun ‘dan samu delay da Jirgin Azman.
Da muka shiga se Allah yasa wajen zaman mu ‘daya. Mukayi dogon hira dashi, har yana min wasa yace idan muka isa Kano ze bani jikan sa ko ‘yar sa.
Sauqan mu ke da wuya, se yace min muje na gaisa da iyalan sa suna jiran mu a waje.
Motoci biyu sukazo ‘daya qirar Marsandi(Mercedes S600) da kuma wata latest AMG.
Duk yaran farare ne masu kyawun halitta. Shi ne yace min lallai ze bani Daulat(ba asalin sunan taba kenan) idan muka sasanta.
Qarshe dai mukayi musanyen number da yaran. Har da ita yarinyar. Ranar da na fara zuwa hira gidan nasha mamaki.
Saboda babu wani abun duniya da babu acikin gidan.
Daulat ta fito waje ta shiga dani cikin parlor.
Naga abu a ranar, wasu irin grapes aka kawo min masu kama da ‘Dom Perignon’, muka fara hira.
Se take ce min Abban mu yana sonka sosai. Yayi hirar ka yafi so a qirga.
Qarshe dai muka gama hira na kwashi tsohuwar Toyota ta na tafi.
Tun daga ranar ban sake komawa ba. Ba wai don yarinyar bata min ba. A’a, class difference din yayi yawa.
Saboda idan ban mai da hankali ba, albashi na da wasu kudaden da nake samu a saya mata Super Wax da designer perfumes ze na qarewa.
Qarshe ina wahala, ita kuma abinda nake yi be ma kai kwatan abinda iyaye suke mata ba.
Dole ne wani lokaci ka duba class din mace matuqar da niyyar aure kake sonta ba da bata lokaci ba!!
Meh zaka iya cewa dangane da labarin da Elder Karofi yabayar akan duba Class din mace kafin kayi maganan aurenta?
Kalli Bidiyon Irin Matan Da Yakamata Ka Aura ⇓