Labaran Yau

Wasu Tsoffin Gwamnoni Sunyi Abota Da Yan Ta’adda Cewar Uba Sani

Wasu tsoffin Gwamnoni sunyi Abota da yan Ta’adda cewar Uba Sani

Gwamnan jihar kaduna, Uba Sani, yayi zargin wasu tsoffin gwamnoni a Arewa maso yamma wajen bata tsarin tsaro a yankin, yayin da suka kulla abota da yan ta’adda.

Sani, bai ambaci sunan gwamna ko daya ba, Amma yayi zargin gwamnonin da daukan matakan da basu dace ba a fanin tsaron cikin gida na jihar, wanda hakan ya taimaka wajen matsalolin da ake ciki yanzu.

“Ina tuna lokacin da jihar kaduna da wasu jihohi na Arewa maso Yamma suka hadu da jihar Neja, dukansu Suna da boda damu, Mun zauna wajen magance matsalar tsaro”. Sani ya bayyana hakan wa channels TV ranan Talata.

“Muna da kwamiti, da kuma Muna ajiye kudade, Muna aiki kusa da kusa da sauran jami’an tsaro, sojin kasa da na sama, da Kuma yan sanda.

“ Wasu daga cikin gwamnonin suka fara zama da yan ta’addan suka karya alaqan yayin da suke tattaunawa dasu Kuma Suna basu kudade da Kuma zama dasu dan yin sulhu” ya kara da cewa.

Gwamnan yace kirkiro da yan sandan jiha shi zai fi wajen magance matsalolin tsaro dake kalubalentar Najeriya. Yace hakan yanada muhimmanci saboda karfin da aka bawa gwamnonin kan tsaro bai da yawa.

Yace yaji dadi kusan duka gwamnonin sun amince da kirkiro yan sandan jiha wanda shine zai kawo cigaba ta fannin tsaro.

Ya ce, “Ina tuna lokacin da nake sanata na kawo dokar kirkiro yan sandan jiha a Majalisan tarayya amma abin ya watse bamu ci nasara ba.

UBA Sani yace a matsayin sa na gwamna zai bada goyon baya wa Majalisan tarayya na goma wajen dawo da maganar kirkiro yan sandan jiha.
Saboda hakan shi zai kawo karshen kalubalen tsaro a kasar.

 

Daily trust ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button