ACF Tayi Allah Wadai Da Yunkurin El-rufai
Kungiyar Tuntuba ta Arewa ACF ta yi fatali da barazanar da gwamnan jihar Kaduna Malaman Nasir Ahmed El-Rufai ya yi na cewa, za su shigo da sojojin haya daga kasar waje tun da Gwamnatin Tarayya ta gaza tabbatar da tsaro a Nijeriya.
Kurarin na El-Rufai dai ya biyo bayan kara samun aukuwar hare-haren ‘yan bindiga a jihar da kuma harin da su ka kai na bam a kan fasinjojin da ke a cikin jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa jihar Kaduna a ranar Litinin data wuce, inda iftila’in ya janyo mutuwar fasinjoji tara da kuma sace wasu da dama.
ACF a cikin sanarwar da Sakatare Janar dinta Murtala Aliyu ya fitar a jiya Lahadi ta yi nuni da cewa, nauyin Gwamnatin Tarayya ne ta samar da tsaro a Nijeriya, inda kungiyar ta yi kira da samar da mafita kan kalubalen na rashin tsaron.