Labaran Yau

Majalisan Dattawa ta Amincewa Tinubu ya zabi Masu Bada shawara Guda Ashirin

Majalisan Dattawa ta Amincewa Tinubu ya zabi Masu Bada shawara Guda Ashirin

Majalisan dattawa ta Amince wa shugaban kasa Bola Tinubu ya zabi masu bada shawara guda Ashirin. Shugaban Majalisan dattawa Ahmed Lawan ya karanta neman ranan talata cikin majalisa, yayin da suka amince wajen zabe ta murya.

Sunayen wanda za’a zaba basu cikin takardan neman kuma ba’a san su waye bane.

“Saboda babu sunayen masu bada shawaran, Zamu amince a nan. Zai iya yiwuwa abu ne Mai muhimmanci matuka” a cewar sa.

Hakan yazo kwanaki kadan bayan Tinubu yayi zaben mukamai na farko.

Ya bada mukami wa tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya SGF.

Shugaban kasa Tinubu ya zabi Shugaban Majalisan tarayya Femi Gbajiamila a matsayin shugaban Ma’aikatan Shugaban kasa da kuma tsohon mataimakin gwamnan jigawa Sanata Ibrahim Hadejia a matsayin mataimakin Shugaban Ma’aikatan Shugaban kasa.

Daily trust ce Ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button