Labaran Yau

Yadda Ake Sarrafa Kunun Gyada Mai Shinkafa, Ayaba, Da Sauran Yanayi Daban Daban

Yadda Ake Sarrafa Kunun Gyada Mai Shinkafa, Ayaba, Da Sauran Yanayi Daban Daban

Assalamu Alaikum, Barkanmu Da Yau, Jami’in Labaranyau Blog ya zauna yakawo cikakken bayani kan yadda ake hada Kunun Gyada wanda zai hana mijinki yimiki kishiya

Dan Samun cikakakkiyar bayani kan Girke Girke, kuyi da hanzari wajen garzayoya shafin mu ta labaranyau dan koyar kala kalar abinci masu dandano Mai fadi.

A yau zamu kawo maku yadda Ake hada kunun gyada guda uku, akwai yadda ake hada kunun gyada calla, yadda zaku hada kunun gyada mai shinkafa daban yake da yadda za a hada kunun gyada mai ayaba. Bayani a saukake. Kuma dai kunu ya danganta da yawan yanda zakiyi.

Bayanin da muka kawo muku za ayi kunu ne na mutum biyu zai kasance a bayanin mu.

Kayan hadin kunun gyada zalla

i. Gyada
ii. Flour ko garin gero
iii. Lemun tsami ko tsamiya
iv. Sugar
v. Madara inda hali

Yadda Za’a Hada;

Yadda Zamu fara kunun gyadan mu dai Zamu samo gyadan kunu mai kyau kofi biyu Sai a soyata sama sama kada a bari ta kone amma idan anaso tayi kamshi.

Bayan ta soyu sai a sauke a bazata a faranti murjeta saboda bayan ya fita sai markada gyadar, zaki iya daka a turmi yayi laushi ko ayi amfani da engine ko kuma idan akwai blender da wutan Nepa ko generator za a iya nikawa yayi laushi sosai.

Bayan an nika gyadar tayi laushi sai a tace a fitar da dussar ko tsakuwan da tayi, sai a samu tukunya a daura a wuta ki sa ruwa dan kadan ba dayawa ba. Sannan in anyi wannan sai daman tsamiyan ya juku ko lemun tsami an matse, sai a kawo kullin kunun geron ko flour din dai dai yanda idan aka sa zai yi kauri, sai a zuba a cikin ruwan gyadan da ke kan wuta Sai a jujjuya yayi kauri yadda ake so, sai a sauke a sa lemun tsami ko jikakkiyar tsamiya in an juya ya dan huce sai a sa sugar.Shikenan kunun gyadar ta hadu, sai zuba a sha.

YADDA AKE KUNUN GYADA MAI SHINKAFA

Kayan Hadin Kunun Gyada Mai shinkafa

i. Gyada
ii. Shinkafa
iii. Sugar
iv. Madara
v. Lemun tsami
vi. Flour ko garin gero

Yadda za’a hada :

Shi Kuma kunun gyada Mai shinkafa Ana hada shi ne in gyara gyadar, a wanke ta, a shanyata ta bushe sai a soyata shima sama sama ki murje ta bawan ya fita,sai a markada da engine ko blender, idan an markado sai a tace da abin tata ko rariya, sai a zuba a tukunya a daura akan a wuta. Kamin nan an dafa shinkafa a kalla Rabin kofi.

ita dafaffiyar shinkafar za a zuba a ciki ana juyawa har ya tafasa sosai sai a dauko flour wanda aka damata da ruwa ya danyi kauri, Sai a zuba ciki Ana juyawa har sai kaurin sa ya kai yadda akeso. Sai a matse lemun tsamin, bayan an sauke ita kunun Sai a zuba lemun tsamin ciki a juya da kyau.

Idan ya huce kadan Sai a zuba madara inda halinta kamin a saka sugar. Ana saka sugar ne in ya huce saboda kar ya tsinke. Sai a zuba a kofi a sha kunun gyada mai shinkafa mai dadin gaske.

YADDA AKE HADA KUNUN GYADA MAI AYABA

Kayan hadin kunun Gyada da Ayaba

i. Gyada
ii. Ayaba
iii. Gero
iv. Sugar
v. Madara

Yadda za a hada:

Ita ma sai an gyara gyadar an soyata dan dai dai Sai a wanko a kai markade ko a markada da blender ko engine. A markada yayi laushi Sai a tace da rariya a Kuma markada ayaba wanda aka bare ta. A zuba tukunya a daura a kan wuta Sai sun dahu ya fara fitar da kumfa.

Ita gyadar da ayaban da tayi kumfa, za a dauko flour ko garin gero wanda aka mai da kulli Sai zuba a cikin kunun Ana juyawa a hankali har sai ya kama jinkinshi yayi kauri yadda ake so Sai a sauke.

Sai a bari ya dan huce kadan kamin a saka sugar da Kuma madara inda hali. Sai a zuba a kofi a sha kunun gyada mai ayaba wanda ke da matukar dadi.

Ko wacce mace yakamata ta san yadda zata rike mijinta da abinci Mai dandano.

Easiest Kunun Gyada Recipe ⇓

Yadda Ake Miyar Taushe (wato miyar gyada)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button