Labaran YauNEWS

Ankama Kimanin Kwayan Tramadol Na Naira Miliyan Dubu Biyar

Ankama Kimanin Kwayan Tramadol Na Naira Miliyan Dubu Biyar

Hukumar yaki da taanadi da  miyagun kwayoyi ta Nijeria [NDLEA] Ta kama Kimanin Kwayan Tramadol Na Naira Miliyan Dubu Biyar wanda adadin yawansu yakai guda miliyan tara da rabi a tashan saukar jirgin sama na Lagos, Abuja da Edo.

Sanarwan ya fitone ta bakin jami’in yada labarai na hukumar MR Femi Babafemi a hedkwatar Hukumar dake binin tarayya Abuja.

Kwayoyin sun hada da katan dari biyu da goma sha hudu 214 na Tramadol da guda dari biyu da ashirin da biyar 225 masu dauke da sunaye daban-daban, inda ya kasance jimla 9, 219, masu dauke da kimanin nauyin kiliogram  6, 384.5 wanda kudinsu yakai naira miliyan dubu biyar N4, 609, 700, 000 ancimma nasaran wannan aikinne tare da hadin gwuiwar hukumar costom.

Miyagun kwayoyin wasu zaa kaisu jihar kano wasu jihar Edo.

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button