NEWSLabaran Yau

Sakon Hon Mubarak Haruna Mai Rakumi Ga Yen Convention – APC

Sakon Hon Mubarak Haruna Mai Rakumi Ga Yen Convention – APC

SAKON BAN GAJIYA GA DAUKACIN AL UMMAR MU DA SUKA HALARCI TARON CONVENTION A ABUJA

Assalamualaikum Bayan sallama irin wadda addinin mu na Islama ya shar’anta mana, ina mai farawa da mika godiya ga Allah da ya kaddari uwar jam’iyyar mu ta APC ta gudanar da taron convention lafiya cikin sauki da nutsuwa.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Hakika wannan yana nuni ne da irin sakon nasara dake gaban mu musamman a babban zaben da muka sanya a gaba na 2023. Ina yiwa yan uwan mu, musamman magoya bayan mu da suka samu halartar wannan taro ban gajiya da kuma fatan sun isa gida lafiya Allah Ya sa haka amin.

Ina kara mika sakon ta’aziyya ga al ummar karamar hukumar Zaki bisa rashin daya daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar mataimakin shugaban jam’iyyar na Zaki, Ubangiji Allah Ya jikansa da rahama amin.

Ina kuma mai jajantawa mutanen mu na karamar hukumar Itas/Gadau da wasu daga jamaare bisa iftila’in da suka hadu dashi a hanyarsu ta komawa gida wadda cikin ikon Allah suka samu nasarar tserewa daga hannun mutane bata gari, Allah Ya kiyaye aukuwar irin wadannan ayyuka a kasar mu Najeriya baki daya amin.

Muna godiya matuka bisa yadda jama’a suke nuna mana goyon baya da soyayya bisa aminta da yadda da suka yi damu, wanda insha Allahu muka ci alwashin zamu cire musu kitse daga wuta matukar Allah Ya bamu dama fiye da wadda muke da ita a halin yanzu. Allah Ya taimaki Jam’iyyar APC, jihar Bauchi dama kasa baki daya amin.

Alhaji Mubarak Haruna (Mai Rakumi) ūüźę 30th Maris 2022.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button