Labaran Yau

Shugaban Sojoji Ya Kaddamar Da Sabon Shirin Kawo Karshen Kashe Kashe A Jihar Plateau

Shugaban Sojoji Ya Kaddamar Da Sabon Shirin Kawo Karshen Kashe Kashe A Jihar Plateau

A ranar Asabar ne babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya kaddamar da Operation Hakorin Damisa domin kawo karshen kashe-kashe da kalubalen tsaro a jihar Filato.

Hafsan sojin ya kuma sake jaddada aniyar rundunar sojin Najeriya na yakar masu aikata miyagun laifuka da suka addabi wasu al’umma a karamar hukumar Mangu da sauran yankunan jihar.

Manjo Janar Lagbaja ya halarci kaddamarwar da kansa a garin Mangu domin kaddamar da ayyukan sojojin da ke karkashin Operation Hakorin Damisa IV a wani bangare na aikin bayar da agajin gaggawa a karkashin rundunar hadin gwiwa ta tsaro, Operation Safe Haven don magance kalubalen tsaro a yankunan kananan hukumomin Mangu, Riyom, da Barkin-Ladi.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Shugaban sojojin ya gargadi sojojin da su mutunta ka’idojin aiki a yayin gudanar da ayyukansu.
Ya kuma yi kira ga ‘yan kasar da ke yankunan da abin ya shafa da su ba sojojin hadin kai tare da bayar da bayanan da suka dace.

Tawagar ta musamman ta kunshi dakaru 300 tare da Motocin Juriya na Makiyaya guda bakwai, Babura, Motocin sintiri na Buffaloes, da Motoci masu sulke.

An samu kashe-kashe da dama a jihar Filato inda akasarin hare-haren ‘yan bindigan yafi faruwa ne a yankin Mangu na jihar ta Plateau.

Shugaban Sojojin Tsaro Na Kasa Ya Dau Alwashin Nuna Bajintar Sojin Najeriya A Fili

Babban hafsan hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa, ya ce a jiya zai inganta kere-kere a cikin rundunar sojojin kasar nan, sannan kuma ya dauke alwashin fito da bajinta ta sojojin na kasa ta hanyar basu jagoranci na gari.

Ya kuma ce rundunar sojin kasar za ta mayar da ‘yan Najeriya abin da za su mayar da hankali kai, sannan zasuyi ayyukan da za su sanya kasa a gaban har ila yau zasu tabbatar sun inganta da kuma kare muhallin kowa.

Ga Karashin Bayanin Shugaban Tsaron Anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button