Dalibar Jami’a ta sadaukar da takaddunta wa mahaifinta daya rasu
Dalibar jami’a mai suna Fatima Ahmad ta kammala bautan kasanta a wannan rukuni, ta kasance jajircecciya wurin gina kai da karatu.
A yau ranar jumu’a dalibar jami’an ta saka hotunanta tare da kawayenta dan murnan gama bautan kasa da karatun da tayi, tayi nuni na kauna ace da kuma kewa da tayi na rashin kasancewan mahifinta dan ganin cikan burinta.
Hakan yana nuni da irin dawainiya da kokarin da mahifinta keyi dan ganin cikon burin nata lokacin da yake raye.
A shafin nata na sada zumunta wato Facebook, Dalibar Jami’an ta sanya hotunan ta tare da takardan shaidan gama bautan kasanta wanda bayanin ta ya kai ga dunbun tausayawa na jama’a.
Bayanin nata tayi cikin harshen turanci wanda ya ka sance haka a hausance:
“Alhamdulillah Alhamdulillah!!! Na sadaukar da takardar shaida ga mahaifina marigayi Dr. Ado Ali Ahmed ningi… nayi fatan yana kusa ya shaida dis day💔💔Allah ya karawa baba daraja a JANNAH..Ameen”
Daliban tagama karatun nata ne a wannan shekara wanda tayi bautan kasan nata ne a cikin garin gombe kuma ta kasance yar Bauchi ce.